Oluremi Tinubu Ta Ba Da Tallafin Naira Miliyan 110 Ga Iyalin 'Yan Wasan Kano da Suka Rasu

…Gwamna Yusuf Ya Kara Tallafin Naira Miliyan 130, Filaye da Sauran Kayan Jin Kai

Uwargidar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba da tallafin naira miliyan 110 ga iyalan 'yan wasan Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a farkon shekarar nan.

Tallafin, wanda aka bayar ta hannun Victim Support Fund, ya bai wa kowanne iyali na mamatan 'yan wasa naira miliyan 5 domin rage musu radadin rashin da suka yi da kuma taimaka musu su farfado da rayuwarsu.

A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Gidan Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan kyauta daga Uwargidar Shugaban Ƙasa a matsayin “wata alama karara ta nuna jin ƙai, kyakkyawan Shugabanci da tausayi ga ɗan Adam.”

A matsayin karin taimako daga gwamnatin jiharsa, Gwamna Yusuf ya sanar da bayar da ƙarin naira miliyan 130. 'Yan wasa goma da suka jikkata sun samu naira miliyan 2 kowannensu da kuma fili, yayin da kowanne iyalin mamatan ta ƙara samun naira miliyan 5.

Tun da farko, gwamnatin jihar ta bayar da naira miliyan 22 a matsayin tallafi, inda aka bai wa kowace iyali na marigayun naira miliyan 1, yayin da masu rauni suka karɓi naira dubu 500 kowannensu.

Wasu daga cikin sauran gudummawar da aka samu sun haɗa da:

Gwamnatin Jihar Ogun – Naira miliyan 32

Gwamnatin Jihar Jigawa – Naira miliyan 20

Injiniya Sagir Koki – Naira miliyan 2.2


Jimillar dukkan tallafin kuɗi da aka bayar ga waɗanda abin ya shafa ya kai naira miliyan 321.2, tare da buhunan shinkafa 30 da filaye da gwamnatin Kano ta bayar.

An raba tallafin nan take ta hannun Akanta Janar na Jihar Kano a wani biki na musamman da aka shirya domin karrama waɗanda suka rasu.

A matsayin tunawa da su, Gwamna Yusuf ya sanar da sauya sunan Kano Sports Institute da ke Karfi zuwa “Kano 22 Athletes Institute”, domin girmama 'yan wasan da suka rasa rayukansu.

Domin tabbatar da gaskiya da bin tsarin gado na Musulunci, an ɗora wa kotunan shari’ar Musulunci alhakin kula da rabon naira 6,709,375 da za a ba kowanne iyali daga cikin iyalan mamatan a matakin farko.

Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Alhaji Baffa Indabawa, shugaban ƙungiyar iyalan waɗanda suka rasu, ya bayyana godiya ta musamman ga Uwargidar Shugaban Ƙasa da Gwamnatin Jihar Kano bisa wannan taimako da ya bayyana a matsayin “ta’aziyya mai taɓa zuciya da girmamawa.”

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki