Waiwaye Adon Tafiya: Daya Daga Cikin Dalilan Da Suka Sa Muke Yakar Yin Zanga-zanga A Kano - Farfesa Salisu Shehu

A shekarar 2003 ne Amerika ta jagoranci mamaye Kasar Iraqi . Wannan aiki na zalunci da ta'addanci ya tunzura Kasashen Musulmi wanda ya sa aka rinka ZANGA-ZANGA da kona tutar Amerika a kasashen Musulmi baki daya. KUMA abin lura da izina shi ne duk wadannan ZANGA-ZANGA basu hana Amerika yin ta'addancin da ta yi niyya ba. Bil hasali ma kara maimaitawa take ta yi, WAMA LIBYA, WA SIRIYA , BI BA'ID.

Wannan dalili ya sa mu ma a Kano aka shirya lacca ta musamman a Masallacin Umar ibn Al'-Khattab (Dangi) wacce kusan dukkan manyan Malamanmu na Kano kamar su Sheikh Isa Waziri, Sheikh Ibrahim Umar Kabo, Sheikh Dr. Aminuddeen Abubakar, Sheikh Ja'afar, Sheikh Yahaya Faruk Chedi , etc Rahimahumullahu duk sun halarta. Daga nan Masallacin aka yi jerin gwano cikin lumana aka bi State Road aka je gidan Gwamnati aka mika takarda ta yin Allah wadai da Kasar Amerika, aka bukaci Gwamnatin Jihar Kano ta isar da takardar ga Ofishin Jakadancin Amerika . Daga nan aka dawo Masallaci lami lafiya kowa ya koma gida. 

Amma kafin Azahar kawai sai rahotanni suka fara fitowa cewa yara matasa marasa tarbiyya suna can suna ta kaiwa hari suna fasa kantina da shagunan mutane a sassa da unguwanni daban - daban a cikin Birnin Kano. Sun yi gagarumar barna ga dukiyoyi da kadarorin al'umma har ma rayuka sun salwanta, kafin a shawo kansu, a magance matsalar. 

Wannan dalili ne ya sa , sama da shekara 20 kenan ko da yaushe, muke kauce ma ZANGA-ZANGA a Kano.

Akasarin yaran da suke zagin Malamai a social media don sun ce kada a yi ZANGA-ZANGA ba a haifesu ba a lokacin. Basu san ne ya faru ba a wancan lokacin .

Daga 2003 zuwa yanzu 2024 shekaru 21 kenan, Birnin Kano ya kara cika , ya batse, kuma matasa marasa aikin yi, marasa tarbiyya sun ninninka na 2003, kuma tsaurin ido da ayyukan laifi (crime and violence) sun habaka, sa'annan kuma uwa-uba ga yaduwar manyan makamai a cikin garuruwanmu (kauyuka da birane) , ga yawan kashe-kashe da rashin tausayi duk sun tsananta, ga daba da jagaliya sun fadada kuma sun gawurta a cikin unguwanni. Ko watannin baya mun ga yanda yan phone snatching suka so su buwayemu. Har wa yau mun ga yanda matasa suka fi karfin jami'an tsaro lokacin rusau, suka rika cin karensu ba babbaka. Idan aka yi kuskuren fitowa ZANGA-ZANGA a Kano, kuma aka yi rashin sa'a matasan nan suka yi hajiacking lamarin, Allah ne kawai ya san yanda akibar abin za ta kasance. 

Ita fitina za a iya sanin farkonta, amma babu wanda zai iya sanin karshenta. MAGANIN KADA A YI, KADA A FARA. 

BANA JIN DUK WANDA YAKE KAUNAR KANO, zai goyi bayan a yi ZANGA-ZANGA a Kano a halin da muke ciki.

ALLAH KAWAR MANA DA FITINA DAGA DUKKAN GARUWANMU NA MUSULMI BAKI DA DAYA

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki