Posts

Air Peace Zai Kwaso Daliban Najeriya Da Suka Makale A Sudan Kyauta

Image
  Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya ce zai kwaso daliban Najeriya da suka makale a kasar Sudan inda yaki ya barke, kyauta zuwa gida. Rikicin shugabanci ya kazance a Sudan a baya-bayan nan, har ta kai ga rufe sararin samaniyar kasar. Akalla daliban Najeriya 5,000 da ke Sudan sun nuna matukar bukatar a dawo da su gida, inda wasu daga cikinsu ke kokarin tsallaka iyaka zuwa kasar Habasha, mai makwabtaka da Sudan. Shugaban kamfanin Ake Peace, llen Onyema, ya sanar da cewa idan ’yan Najeriya da ke Sudan za su iya tsallaka iyaka zuwa kasashen makwabtakan Sudan, to kamfaninsa zai kwaso su zuwa gida a kyauta. Ya ce aikin kwaso su ya wuce a bar wa gwamnati ita kadai, saboda bai kamata a yi asarar dan Najeriya ko daya ba a rikicin na Sudan. Gwamnatin Tarayya dai ta yi alkawarin ranar Talata za ta fara kwaso ’yan Najeriyan ta kasar Habasha. Wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta ce Ma’aikatarta Harkokin Kasashen Waje na aiki da gwamantin kasar Habasha, domin amfani da sara

Sarkin Kano Ya Bukaci Gwamnati Ta Samar Da Wata Hanyar Da Al'uma Zasu Samu Saukin Rayuwa

Image
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah gidan Gwamnatin jihar Kano a hawan Nassarawa da ya gabatar yau Lahadi a cigaba da gudanar da haye hayen sallah karama. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Sarkin yace sakamako matsin rayuwa da ake fama da ita akwai bukatar Gwamnati da mawadata su tallafawa marasa shi domin samun saukin gudanar da al'amuran rayuwarsu. Ya kuma tunasar da al'uma shirin gwamnati na Kidayar al'uma da za'a gudanar a dukkanin fadin kasar nan inda ya bukaci al'uma dasu tabbatar an kidayasu a lokacin gudanar da aikin kidayar. Mai Martaba Sarkin godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da Tsaro da Zaman lafiya inda ya godewa Malamai da limamai wajan gudanar da addu'oi domin dorewar Zaman lafiya a jihar Kano. Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al'uma su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya yace duk wasu aikace aikac

Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni Sama Da Dubu Hudu Afuwa A Cikin Shekaru Takwas

Image
  Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi afuwa ga fursunoni dubu hudu da goma sha uku a cikin shekaru takwas a fadin gidajen gyaran hali na Kano.  Haka kuma a cikin shekaru takwas gwamnatinmu ta biyan tara da diyya ga fursunonin da suka kai naira miliyan hudu da dubu dari tara da arba’in da tara.  Gwamnan wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana haka a lokacin da ya yi afuwa ga fursunoni 43 da suka aikata laifuka daban-daban kuma suke zaune a gidan yari, a yayin bikin karamar Sallah da aka yi a gidan yari na Goron Dutse. Ganduje ya jaddada cewa ’yanci shi ne komai na rayuwar dan Adam, ya yi kira ga fursunonin da aka yi wa afuwar da su nuna kyawawan halaye a duk inda suka samu kansu a cikin al’umma. A jawabinsa Kwanturola na hukumar gyaran jiki a jihar kano, Suleiman Muhammad Inuwa ya bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na yin afuwa ga fursunonin da biyan tara, diyya ya taimaka wajen rag

Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Gudanar Da Taron Shan Ruwa Na Mutum Dubu Biyu

Image
Zababben Dan majalisar  tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji) ya jagoranci taron shan ruwa da al'umar Kiru da Bebeji mutane 2000 a gidansa dake garin Kofa. Bayan buda baki Kofa ya jagoranci mahalatta wannan taro Sallah.  Taron shan ruwan ya sami halartar Dagatai, Limamai, 'Yan siyasa, da sauran mutane daban-daban dake mazabarsa ta dan majalisar tarayya  Yayin taron, anyi amfani da wannan dama wajen yi wa Zababben Dan Majalisar Tarayyar, Alhaji Abdulmumin Jibrin Kofa addu'a da  Gwamna jihar Kano mai jiran rantsuwa Injiniya Abba Kabir . Yusif tare da Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Haka kuma an roki madaukakin Sarki Allah ya dauwamar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jahar Kano da ma Najeriya baki daya

Fiye da mutane 85 sun mutu a turmutsitsin rabon kudi a Yemen

Image
  Akalla mutane 85 suka mutu, wasu daruruwa kuma suka jikkata, sakamakon tirmtsitsi da aka yi yayin wani taron raba kudade da aka yi a Sanaa, babban birnin kasar kasar Yemen da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Houthi. Ya zuwa yanzu mutane 3 aka tsare bisa zarginsu da hannu wajen haddasa tirmitsitsin da sanyin safiyar ranar Alhamis, bayan da daruruwan mutane suka taru a wata makaranta domin karbar kyautar kudin Riyal din kasar ta Yemen 5,000, kwatankwacin dalar Amurka 8 da ake bai wa mutum guda guda, a daidai lokacin da watan Ramadan mai alfarma ya zo karshe. Hotunan bidiyo sun nuna yadda mutanen da mummunan cinkoson ya rutsa da su, suka rika tsala ihu da neman ceto sakamakon kasa motsawar da suka yi, yayin da wasu tsiraru suka rika yunkurin fitar da mutanen da suka ji rauni. Wasu hotunan bidiyon kuwa, sun nuna gawarwakin wasu daga cikin wadanda tirmitsitsin ya rutsa da su ne yashe a kasa, sai kuma tarin takalma da sauran nau’ikan tufafin da aka yi watsi da su, yayin da kuma wani mai binc

Labari Da Dumiduminsa: An Wa Watan Sallah A Saudiyya

Image
  Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023. An ga watan ne a yankin Tumair na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana, hakan na nufin Saudiyya ta kammala azumin Ramadan 29. Gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu zai zama 1 ga watan Shawwal.

Abu bakwai da ya kamata ku yi don tafiya sallar Idi

Image
Sallar Idin ƙaramar salla Ibada ce da Allah Ya shar'anta a matsayin kammala Ibada ta azumin watan Ramadan. Sallar Idi na ɗaya daga cikin sunnoni masu ƙarfi a addinin musulunci wadda ake yi sau biyu a shekara wato, ƙaramar salla da babbar salla. Don haka ne ma sallar idin ke buƙatar wasu abubuwa domin yin guzuri a tafiya zuwa masallacin idin. Dakta Muhammad Nazifi Inuwa wani malamin addini ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya bayyana jerin abubuwan da ya kamata mutum ya yi kafin tafiya sallar idi. Wankan Idi Wankan Idi ɗaya ne daga cikin wanka na sunnah a addinin musulunci wanda ake yi sau biyu a shekara. Dakta Muhammad Nazifi Inuwa ya ce an so duk mai tafiya masallacin idi ya gabatar da wankan Idi, domin dacewe da sunnah. Dangane da wankan, dakta Nazifi ya ce mutum zai iya yin wanka na soso da sabulu domin tsaftace jikinsa, sannan daga baya kuma sai ya yi wankan idin, domin dacewa da ladan sunnar wankan. Haka kuma malamin ya ce sigar wankan iri ɗaya ne da na saura

INEC Ta Bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jahar Adamawa

Image
Hukumar zaɓe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin taƙaddama. Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri'a, 430, 861. Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a, 398, 788. Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa'adi na biyu. Da yammacin Talata ne, jami'in sanar da sakamako, Farfesa Mohammed Mele cikin rakiyar wasu manyan jami'an INEC na ƙasa, ya isa zauren karɓar sakamako da ke Yola, inda ya ci gaba da aikin tattara sakamakon ƙananan hukumomin da suka rage. A ranar 15 ga watan Afrilu ne, hukumar zaɓe ta gudanar da cikon zaɓen cikin wasu rumfuna da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 20. An sake kaɗa ƙuri'u ne a tashoshin zaɓe 69. Sakamakon zaɓen da aka ƙarasa ya nuna cewa 'yar takarar

LABARI DA DUMIDUMINSA : INEC Ta Dauki Matsaya Dangane Da Zaben Adamawa

Image
A taronta na yau, 18 ga Afrilu, 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, ta tattauna batutuwan da suka taso daga zaben Gwamnan Adamawa inda ta yanke shawarar: 1. Rubuta takarda zuwa ga Sufeto-Janar na 'yan sanda domin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da yiwuwar gurfanar da Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa, Barr. Hudu Yunusa Ari. 2. Ya bukaci sakataren gwamnatin tarayya da ya jawo hankalin hukumar da ke nadawa kan rashin da'a na REC don ci gaba da daukar mataki. 3. Za a ci gaba da tattarawa a daidai lokacin da Jami'in da jami'in tattara sakamakon ya amince Cikakken bayani zai biyo baya nan ba da jimawa ba. INEC 

Yau INEC Za Ta Taron Gaggawa Kan Zaben Adamawa

Image
A yau Talata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar ta taron gaggawa da ta kira kan dambarwar sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya tayar da kura. Daga taron ne za a ji shawarar da INEC ta yanke a game da sakamakon zaben gwamnan, wanda a ranar Lahadi hukumar ta dakatar da tattarawa saboda rikicin da ya dabaibaye shi. A ranar Litinin hukumar ta dakatar da Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus Ari, saboda ya yi gaban kansa wajen ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC a matsayin zababbiyar gwamna, alhali ba a kammala tattara sakamakon zaben ba. Lamarin dai ya yamutsa hazo, amma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda yake neman a zaben a Jam’iyyar PDP, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, domin INEC za ta dauki matakin da ya dace. Tuni dai Fintiri da PDP da kungiyoyin kare dimokuradiyya suka yi tir da abin da kwamishinan zaben ya yi, inda suka bukaci INEC ta dauki mataki a kan wannan kwamacala. Rikicin zaben ya dauki sabon