Gwamnan Kano Ya Sauke Hadimansa Guda Biyu Daga Mukaminsu

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta amince da korar manyan mataimaka biyu (Senior Special Assistants) nan take, bayan samun shaidu masu karfi daga rahotannin kwamitocin bincike da aka kafa kan wasu zarge-zargen aikata laifuka daban-daban.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar.

A cikin mataki mai tsauri, Gwamna Abba ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, Mai taimaka masa na musammam kan Kan Hada kawunan yan siyasa bayan wani kwamitin bincike na musamman ya same shi da hannu wajen belin wani sanannen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu, inda shaidar da Sharada ya bayar da kansa gaban kwamitin ta tabbatar da rawar da ya taka a wannan mataki na bayar da beli.

A wasikar da Sakataren Gwamnati ya fitar a ranar Juma’a, 8 ga Agusta, 2025, an umarci Sharada da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga Babban Sakataren  na Sashen Bincike, Kimantawa da Harkokin Siyasa (REPA) a ofishin Sakataren Gwamnati kafin karshen lokacin aiki ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025.

Haka kuma, an gargade shi da kada ya sake yin ikirarin kasancewa jami’i  na gwamnati.

Haka nan, Gwamna Abba ya sallami Tasiu Adamu Al’amin Roba, Babban mataimaki na musammam a Ofishin Majalisar Zartarwa (Cabinet Office), bayan kama shi yana sake nade hatsi na Tallafin rage radadi a wani rumbun a Sharada a shekarar 2024.

Roba ya riga ya gurfana a kotu inda ake tuhumarsa da laifin sata da kuma hada baki wajen karkatar da dukiyar gwamnati.

Haka kuma, an umarce shi da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsa, ciki har da katin shaidar aiki, kafin ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, tare da gargadin kada ya sake yin ikirarin kasancewa jami’in gwamnati.

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar ta wanke Mai bawa Gwamna kan harkokin Shawara kan Hanyoyin Ruwa, Hon. Musa Ado Tsamiya, bayan kwamitin bincike ya tabbatar da cewa bai da hannu a dukkan zarge-zargen da ake masa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tabbatar da ladabi, gaskiya da rashin sassauci kan cin hanci da rashawa, tare da gargadin cewa dukkan jami’an gwamnati su tabbatar suna aiki da nagarta a aikinsu da kuma rayuwarsu ta kashin kai.

Ta wannan sanarwa, an shawarci jama’a da kada su yi hulÉ—a da wadannan mataimaka biyu da aka kora kan duk wani lamari da ya shafi gwamnatin Jihar Kano, domin duk wanda ya yi hakan, to ya rage nasa.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki