AHMSP Tayi Martani Ga Rahoton Da Ba A Tabbatar Ba Kan Shugaban NAHCON, Ta Bukaci Jaridu Su Daina Wallafa Labaran Karya
Kungiyar Ƙwararrun ‘Yan Jarida Masu Tallafawa Aikin Haji (AHMSP) ta yi watsi da rahoton da wata kafar labarai, News Point Nigeria, ta wallafa a ranar 14 ga Oktoba, 2025, karkashin jagorancin edita Mista Farouq Abbas, wanda ya shafi ofishin Shugaban Hukumar Kula da Haji ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman.
AHMSP ta bayyana cewa rahoton cike yake da bayanan da ba a tabbatar da su ba, tare da nuna son zuciya da rashin bin ka’idojin aikin jarida, wanda hakan ke iya gurbata sahihancin aikin labarai musamman a fagen da ya shafi Hajj da Umrah.
A cewar kungiyar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman yana gudanar da ayyukansa cikin gaskiya, doka, da tsari, ba tare da wani laifi ko take haddi ba. Dukkan ayyukan hukumar daga rabon ma’aikata, gyaran farashin Hajj, har zuwa gudanar da ayyuka suna tafiya ne bisa tsarin NAHCON da doka ta tanada.
Kungiyar ta bayyana cewa “ikrarorin rashin gaskiya” da rahoton ya bayar ba su da hujjar da za ta tabbatar da su. Haka kuma, ta ce bai dace kafar labarai ta rika yada bayanan da ba a tabbatar da su ba daga shafukan sada zumunta domin son kai ko siyasa.
AHMSP ta jaddada cewa shugaban NAHCON bai taba bayar da umarni ko goyon bayan wata magana da za ta kai hari ga jami’an gwamnati ko wata hukuma ba.
“Rahotannin da ke nuni da hakan su ne karairayi tsantsa,” in ji kungiyar.
Ta kuma tabbatar cewa duk wani bincike daga hukumomin tsaro ko yaki da cin hanci ke yi, Farfesa Pakistan na bayar da hadin kai dari bisa dari, kuma har yanzu babu wata tuhuma da aka tabbatar a kansa.
A karshe, AHMSP ta yi kira ga ‘yan jarida da kafafen yada labarai da su koma ga abin da aka tabbatar kafin wallafa labarai, tare da gujewa rahotanni marasa tushe da ke iya lalata martabar shugabanni da hukumomin gwamnati.
Kungiyar ta nanata goyon bayanta ga aikin jarida mai gaskiya, daidaito, da bin ka’ida tana mai cewa: “Lokaci ne da jaridu su dawo kan turbar gaskiya, ba turbar son rai ba.”