Akwai yiwuwar a soma cire tallafin fetur a watan Afrilu - Gwamnatin Najeriya
Akwai yiwuwar gwamnatin tarayyar Najeriya ta soma cire tallafin man fetur daga Afrilun 2023, wato watanni uku kafin yadda ainahin lokacin da aka yi niyyar cire tallafin a baya. Ministar kuɗi da kasafi Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wata hira ta musamman da ta yi da gidan talabijin na Arise a yayin wani taro na tattalin arzikin duniya a Switzerland. "Abin da ya fi shi ne wannan gwamnatin watakila ta soma cire tallafi a farkon zango na biyu na wannan shekara saboda zai fi nagarta idan aka cire a hankali a maimakon a jira a cire shi baki ɗaya," in ji ministar. Ta bayyana cewa duka ƴan takarar shugaban ƙasar Najeriya a lokutan yaƙin neman zaɓensu duk suna da ra'ayin cire wannan tallafin Bayan ƙara wa'adin watanni 18, gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira tiriliyan 3.35 kan tallafin mai daga Janairu zuwa Yunin 2023. Wannan ƙarin wa'adin da aka yi ya janyo muhawara matuƙa kan irin kuɗin da za a kashe sakamakon ana ganin cewa zai ƙara giɓi a kasafin kuɗi wanda kum